Bayani game da Nairobin Kasar, Kenya
Nairobi babban birnin kasar Kenya ne, daya daga cikin birane masu tsari na zamani a kasar. Kasancewar sa daya daga cikin garuruwa mai cike da kwazo a Afrika, Nairobi ya samu ci gaba a bangaren ciniki da Sufuri da harkokin sana’a.
Birnin yana da yawan mutane sama da miliyan 4 da baki daga wasu kasashen da suka mallaki manyan kamfanonin kasashen waje da ma’aikatu da ofisoshin jakadanci da kungiyoyi masu zaman kansu sun zama tushe a birnin.
Amatsayin sa na kofar shiga kasar Kenya da yankin gabashin Afrika, akwai manyan kantinan siyayya bila adadin da wuraren shakatawa da wuraren cin abinci da kuma Otel-Otel a Nairobi.
Otel-Otel mafi kyau dake Nairobi
Akwai manyan Otel na gani na fada nau’in 5 star dake tsakiyar birnin Nairobi Otel din Serena da SarovaPanafric. Ga matafiya da su kayyade guzurinsu suke neman Otel-Otel masu araha kana iya sauka a Masaukin Masera ko a Otel din Nairobi Glory Palace dake kan hanyar Mombasa, za ka samu Otel-Otel da dama kusa da hanyar filin tashin jiragen sama na Nairobi kamar su Otel din Panarida kuma Otel din 67 Airport.
Da Jumia Travel, Abinda yakamata kayi kawai shi ne ka zabarwa kanka masauki mafi kyau acikin jerin sunayen dukkanin Otel-Otel dake Nairobi kama daga masu araha zuwa manya masu tsada.Kana iya ganin;
Otel-Otel mafi kyau nau’in 5star dake Nairobi
Otel-Otel mafi kyau nau’in 3 star dake Nairobi
Otel-Otel masu saukin kudi dake Nairobi
Manyan Otel-Otel dake Nairobi har da tsarin dauko bako daga filin tashin jiragen sama